9 Agusta 2021 - 14:42
Najeriya Ta Sanar Da Dakatar Da Ci Gaba Kashi Na Biyu Na Rigakafin Korona A Кasar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da dakatar da ci gaba da allurar rigakafin korona kashi na biyu da ake yi a ƙasar, a daidai lokacin da cutar ta ke ci gaba da yaɗuwa a ɓangarori daban-daban na ƙasar.

ABNA24 : Hakan kuwa yana cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa ce da shugaban yaɗa labarai a ofishin sakataren gwamnatin ƙasar, Willie Bassey, inda ya ce an dakatar da kashi na biyu na rigakafin Koronan wanda a baya aka shirya za a fara shi a gobe Talata.

Sanarwa ta ci gaba da cewa a nan gaba za a sanar da lokacin da za dawo da rigakafin duk kuwa da cewa ba ta faɗi cikakken bayani kan dalilan ɗage ci gaba da yin allurar rigakafin koronan ba.

Hakan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriyar take ci gaba da fuskantar ƙaruwar waɗanda suke kamuwa da kuma mutuwa sakamakon ɓullar cutar musamman nau'i na uku na cutar da ake kira da Delta, inda alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta ƙasar ta fitar ranar Lahadin nan sun nuna cewa ƙarin mutum 471 sun kamu da cutar ta korona.

Ya zuwa yanzu dai gaba ɗaya adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya ya kai 178,086sai mutum 2,187 da suka rasu.

342/